Site icon GMLyrics

Ina Misalan Daraja Da Ban Mamaki

Ina Misalan Daraja Da Ban Mamaki

Ina Misalan Daraja Da Ban Mamaki

1) Ina misalan daraja da ban mamaki da
Jamalinka ya bayyana, ya Allah, haskena!

2) Ya Allahna Madauwami, kwarjininka ya sa
In yi maka sujada fa a cikin zuciyata.

3) In ƙaunace ka kullum kuwa, mai iko duka ne, Don ka yarda ka zo guna, ka nemi ƙaunata.

4) Ba wani uba na duniya, ba wata uwa kuwa,
Da za su iya renonmu yadda ka ke mana.

5) Sai abu ɗaya na ke so, in zauna gabanka,
In ga jamalin haskenka, in dinga sujada.

6) In yi shelar sunanka dai, in riƙa tunani
Yadda ka ƙaunace ni kuwa, ya Allah mai jinƙai.

7) Ina misalin daraja da ban mamaki kuwa
Na tsarin dukan hikima wadda ka ayana.

Exit mobile version