Site icon GMLyrics

Zo, mu yabi ƙaunar Yesu

Zo, mu yabi ƙaunar Yesu

1) Zo, mu yabi ƙaunar Yesu,
Jinƙansa da alherinsa.
Yana shirya mana wuri
Cikin Sama gun Uban.

KORUS
Can a Sama, wurin Yesu,
Masu bi za su taru wurinsa
Za mu rera waƙa,
Mu yabi girman sunansa

2) Lokacin da mu ke nan a duniya,
Ƴar wahala mu ke sha,
Amma ran da za mu Sama
Farin ciki za mu yi.

Korus

3) Bi shi nan da dukan zuciya,
Yi aniya cikin aikinsa.
Za mu manta da wahala
In mun shiga mulkinsa.

Korus

4) Gaba dai, mu Masu Binsa,
Har mu ga Mai Cetonmu.
Wata rana ƙofar Sama
Za ta buɗe dominmu.

Korus

Exit mobile version