Ubanginmu, Mai Ceto
1) Ubanginmu, Mai Ceto,
Don zumunta ne muka zo.
A duniyan nan sai sakewa,
Wurinka fa sai hutawa.
2) Tun jiya, yau, har abada,
Madauwami ne sunanka!
Kai ne ka kafa duniyan nan,
Kai ne mai shirya gida can.
3) Almasihu, Cetonmu,
Ba mu da wani taimako,
Amma ƙaunarka cikakkiya,
Ita ce garkuwar ƴaƴanka.
4) Ƙaunarka ! har wa yau ta tsaya
Da, ka ɗanɗana mutuwa.
Can bisa kursiyin Allahnmu,
Yanzu ka rayu dominmu.
5) Yabo, daraja, godiya
Gare ka Yesu Ɗan Allah!
Ka cika mu da Ruhunka,
Ya koya mana nufinka.
Leave a Reply