Site icon GMLyrics

Tun da Farkon Hasken Safe

Tun da Farkon Hasken Safe

Tun da Farkon Hasken Safe
1)Tun da farkon hasken safe,
Ko ka yi addu’a
Cikin sunan Yesu Kristi,
Ka yi roƙo har ka sami
Taimakonka yau?

KORUS
Yin addu’a dai zai ba mu
Albarka ba iyaka.
Sai ka riƙa yin addu’a
Kowace sa’a.

2) Lokacin zuwan jaraba,
Ko ka yi addu’a
Don ka sami ikon Allah,
Ruhunsa ya taimake ka
Har da nasara?

Korus

3) Lokacin da ka ke fushi
Ko ka yi addu’a
Kada Shaiɗan ya rinjaya
Har ya sa ka yin tuntuƃe
Cikin fushinka?

Korus

4) Cikin tsanani da ba’a
Ko ka yi addu’a,
Ko ka jure, kana roƙo
Har ka sami hutun ranka
Cikin Almasihu?

Korus

Exit mobile version