Verse 1
Ruhun iko, zo gare mu,
Mun ga kasawarmu yau.
Rashin jinkai, rashin kauna
Rashin musun kanmu ma.
Chorus
Sai ka zo, ka tsarkake mu
Daga dukan kasawa.
Muna jira, muna jira
Tsarkake mu duk yanzu.
Verse 2
Ruhun sani, zo gare mu,
Akwai duhu cikinmu.
Sanasshe mu, koya mana
Hanyar tsarkakewar rai.
Verse 3
Ruhun wuta, zo gare mu,
Kone duk muguntarmu
Har mu zama mutanenka,
Cikin dukan gaskiya.
Verse 4
Ruhun haske da addu’a,
Bi da mu, ka karfafa.
Muna bege, muna bege
Har mu sami nasara.
Verse 5
Ruhun kauna, zo gare mu,
Sai ka yafe mu yanzu.
Muna jira, muna kuka,
Amsa dai addu’armu.
Verse 6
‘Yanuwa, ku yafa Yesu,
Yafa sabon hali kuwa
Yafa kuma zuciyar tausayi,
Ladabi da jurewa.
Verse 7
Ruhun Kristi, ni na gode,
Kana nan a zuciya,
Mallake ni, mallake ni
Daga yau har abada.