Skip to content
Home » Hausa Hymns » Ran da Ubangiji za ya dawo

Ran da Ubangiji za ya dawo

  1) Ran da Ubangiji za ya dawo
  Don ya karƃi Masu Bi,
  Ko za ya iske ka kana tsaro?
  Ko fitilarka ‘na ci?

  KORUS
  Sai dai ka tabbata ka yi shiri
  Ko an kira ka yanzu,
  Domin ka sadu da Ubangiji,
  Lalle, lalle ya fi kome kyau.

  2) Ran da ya tafi, ya ba ka aiki
  Wanda za ka dinga yi.
  Ko ka yi aikinsa da aminci?
  Ko ka ƃata lokaci?

  Korus
  3) Ran da ka mayai da talents naka,
  “Bawan kirki,” za ya ce?
  “Shiga ka huta a cikin gida,”
  Ko, “Kai mugun bawa ne”?

  Korus
  4) Ba daman shiri idan ka mutu,
  Ba ka iya ruɗinsa.
  Kada ka kasa ka shige hutu
  Domin rashin gaskiya.

  Korus

  Leave a Reply

  Your email address will not be published. Required fields are marked *