Na Ji Kiranka Yanzu, Ya Ubangijina
1) Na ji kiranka yanzu, ya Ubangijina.
A cikin jininka, Yesu, ka wanke zuciyata.
KORUS
Ubangijina, ga ni nan, na zo,
Sai ka ji addu’ata, ka ba ni taimako.
2) Ko na zo da zunubi, da rashin ƙarfina,
Na sani kai ba za ka ƙi ka tsarkake ni ba.
Korus
3) A wurinka kaɗai akwai murna sosai.
Kai ne ka ba ni kwanciyar rai da sanin gaskiya.
Korus
4) Ina so in ci gaba, in zama cikakke,
In koyi irin halinka, in ɗauki giciye.
Korus
Leave a Reply