Muna Cikin Tafiya, Tafiya Zuwa Sama
1) Muna cikin tafiya, tafiya zuwa sama.
Menene za mu ƙunsa a hannunwanmu
don saduwa da Yesu?
Saduwarmu, menene za mu ƙunsa
A hannunwanmu don saduwa da Yesu?
2) Mai yin zina, menen za ka ƙunsa
A hannunwanka don saduwa da Yesu?
Mai yin sata, kana cikin tafiya
Tafiya zuwa sama, menene za ka ƙunsa
A hannunwanka don saduwa da Yesu
3) Mai yin tsafi, menene za ka ƙunsa a
Hannunwanka don saduwa da Yesu?
Mai yin ƙarya, kana cikin tafiya,
Tafiya zuwa sama, menene za ka
Ƙunsa a hannunwanka don saduwa da Yesu ?
4) Mai kormoto, menene za ka ƙunsa
a Hannunwanka don saduwa da Yesu?
Mai yin fushi kana cikin tafiya,
Tafiya zuwa sama, menene za ka
Ƙunsa a hannunwanka don saduwa da Yesu?
5) Mai yi gulma, menene za ka ƙunsa
a hannunwanka don saduwa da Yesu?
Mai yin kisa, kana cikin tafiya,
Tafiya zuwa sama, Menene za ka ƙunsa
a hannunwanka don saduwa da Yesu ?
6) Mai maza biyu, menene za ki ƙunsa
a hannunwanki don saduwa da Yesu?
Mai-mata biyu. kana cikin tafiya,
Tafiya zuwa sama, menene za ka ƙunsa
a hannunwanka don saduwa da Yesu?
Leave a Reply