Skip to content
Home » Aure Na Masu Bi, Aure Ne Mai Tsarki

Aure Na Masu Bi, Aure Ne Mai Tsarki

  Aure Na Masu Bi, Aure Ne Mai Tsarki

  1) Aure na masu bi aure ne mai tsarki, ku ƙaunace juna har abada
  Ubangiji Allah shi ne ya kafa aure ya ce mu yi aure a duniya

  KORUS
  Ku zama ɗaya cikin zamanku, Amarya yi bayayya
  Ango ka ƙaunaceta gidan ku zai zama da Albarka

  2) Ango na murmurshi, Amarya na murmurshi, dono yau suna cikin alkawali
  Mu masubi duka muna tayaku murna mune shaidun wannan aure a yau.

  Korus

  3) Ku ba juna shawara juna yin addu’a, ku zuba ido ga Yesu Kristi,
  Ko cikin wahala ko cikin jin daɗi ku kasance da ƙaunan junan ku.

  Korus

  4) Macen kirki takan faranta ran mijinta mara kirki takan zama ciwo
  Amarya ki zama mai faranta ran mijinki, mijinki zai kasance da murna.

  Korus

  5) Samari da ƴan mata sai ku yi addu’a don ku yi nasara da magabci.
  Mu masu bi duka muna yin addu’a Ubangiji y baku nasara.

  Korus

  Leave a Reply

  Your email address will not be published. Required fields are marked *