Site icon GMLyrics

Almasihu, hasken duniya

Almasihu, hasken duniya

1) Almasihu, hasken duniya,
Begen dukan masu rai,
Yesu Rasul, Kalmar Allah,
Tun fiI azal kai kaɗai.
[Kai kaɗai madauwami ne,
Kai kaɗai maɗaukaki.] 2x

2) Kai ka ajiye rigar mulki,
Ka bar duk don cetonmu.
Zafin mutuwa ba ka ƙi ba,
Duk ka sha don ƙaunarmu.
[Karƃi yabo, karƃi mulki,
Naka ne har abada.] 2x

3) Mutuwa ta rasa iko
Bisanka, Mai Nasara.
Lahira ta buɗe ƙofa,
Ka shiga, har ka fita.
[An ɗauke ka can a Sama,
Aikinka ka gama nan.] 2x

4) Duk jama’a suna jiran
Zuwanka, ya Almasihu,
Duk Ekklesiya tana zarnan
Kewarka, Mai Cetonta.
[Zo da sauri, muna bege,
Zo, mu dinga ganinka.] 2x

5) Al’ummai, ku kasa kunne,
Shi ne Ubangijinku.
Ruhun Allah, jawo mutane
Zuwa sawun Mai Cetonsu,
[Ɗan Maryamu, Tsatson Dawuda,
Ibnu Llahi, Ɗan Mutum.] 2x

Exit mobile version