Skip to content
Home » Hausa Hymns » Albarka tana kan mutum wanda bai ratse ba

Albarka tana kan mutum wanda bai ratse ba

    1) Albarka tana kan mutum wanda bai ratse ba,
    Wanda bai tsaya a hanya ta masu zunubi ba.

    2) A wurin masu ba’a, shi ba ya kan zauna ba,
    Maganar Allah ya ke bi dare da rana kuwa.

    3) Misalin itace ne shi a bakin ruwaye,
    Zai ba da ƴaƴa lotonsa, yaushi kuwa ba ya yi.

    4) Duk aikinsa da ya ke yi, albarka tana kai.
    Miyagu kamar ƙaiƙai ne, iska zai ture su.

    5) Ranar shari’a, miyagu ba za su tsaya ba,
    Ko kuwa su masu zunubi a gidan adalai.

    6) Ubangijinmu kuwa ya san tafiyar adalai.
    Amma tafarkin miyagu lalle zai lalace.

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *