Skip to content
Home » 3jwise » Akwai sunan nan mai daɗi wanda ba mai kamarsa

Akwai sunan nan mai daɗi wanda ba mai kamarsa

  1) Akwai sunan nan mai daɗi wanda ba mai kamarsa,
  Wato sunan Ubangiji, begen dukan Masu Bi.

  KORUS
  Sunan nan, Yesu ne, sunansa da daɗin ji,
  Sunan nan, Yesu ne, begen dukan Masu Bi.

  2) Tun da na ji sunan Yesu, murna na ke yi sosai.
  Wurinsa na sami ceto, gafara da kwanciyar rai.

  Korus
  3) Cikin sunan nan mai girma, a ke samun ceto fa,
  Cikinsa a ke sujada, cikinsa a ke addu’a.

  Korus

  4) Sunan nan ya buɗe ƙofa, zuwa Allah Ubansa,
  Gama ban da sunan Yesu, Allah ba za ya ji mu ba.

  Korus

  1 thought on “Akwai sunan nan mai daɗi wanda ba mai kamarsa”

  Leave a Reply

  Your email address will not be published. Required fields are marked *