1) A cikin duniyan nan yanzu,
Ya Ubanjiji, bi da mu.
Akwai jaraba ko’ina,
Ka bi da mu da Ruhunka.
KORUS
Ya Ubangiji, Mai Ceto,
In ban da kai, ba taimako,
Ka koya mana nufinka,
Ka bi da mu da Ruhunka.
2) Ga aiki yana jiranmu,
Ga tumakinka, ƃatattu,
Mu je mu kawo su yanzu,
Ka bi da mu da Ruhunka.
Korus
3) In za mu shiga yaƙinka,
Mu yi kokawa da magauta,
Ka ƙarfafa ƴan yaƙinka
Ka bi da mu da Ruhunka.
Korus
4) Idan mun gama aikinka,
Ka kira mu ga hutawa.
Ka bi da mu da Ruhunka,
Ka kai mu Sama lafiya.
Korus
Leave a Reply