• Skip to main content
  • Skip to primary sidebar
  • Privacy Policy

GMLyrics

Gospel and Christian Music Lyrics. Submit, Print and Download Christian and Gospel Music Lyrics By Artiste

You are here: Home / Hausa Hymns / Da Duniyan Nan da Girmanta da Yawan Daɗin Rai

Da Duniyan Nan da Girmanta da Yawan Daɗin Rai

Da Duniyan Nan da Girmanta da Yawan Daɗin Rai

1) Da duniyan nan da girmanta da yawan daɗin rai
Su dā sun jarabce ni, sun kama ni sosai.
Amma da dukan daɗinsu ban ƙoshi ba daɗai,
Gama raina ba ya ƙoshi in ban da kai kaɗai.
Yesu, Yesu, Yesu Gurasar Rai,
Ban yarda ba, ban yarda ba a raba ni da kai.

2) Ko raina ya matsu fa, ko kewa na ke ji,
Ko ina shan wahala, ko ciwo na ke yi,
Ni sai in nemi Yesu, shi ne ya ce in zo,
In faɗa masa duka, in roƙi taimako.
Yesu, Yesu, Yesu Mai Taimako,
Ban yarda ba, ban yarda ba a raba ni da kai

3) Alkawarin Mai Cetonmu ba za ya tashi ba.
Mai zuwa ba a ƙinsa in ya zo da gaskiya.
Ina dalilin zafin zuciya, babu hutawa?
Ga Yesu yana jira, ba iyakar tausayi.
Yesu, Yesu, Yesu mai ƙaunata,
Ban yarda ba, ban yarda ba a raba ni da kai.

Check Out

  • Ina Misalan Daraja Da Ban Mamaki
  • Bethlehem Ephratha
  • Aure Na Masu Bi, Aure Ne Mai Tsarki
  • Sai Godiya
  • Muna Cikin Tafiya, Tafiya Zuwa Sama
  • Alherin Ubangijina Abin Mamaki Ne
  • Ni Sojan Yesu Ne
  • Mun Gode
  • Godiya Iye
  • Ba Gajiya

Search For Lyrics

Reader Interactions

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Primary Sidebar

SEARCH FOR OTHER LYRICS

Recent Posts

  • Ojone Martha – My Story Lyrics
  • EmmaOMG & The OhEmGee Band – Oba Ni Jesu Lyrics
  • Becky Adjodi – None Like You Lyrics
  • Ani John King – King of the Earth Lyrics
  • Jaymikee – Dide (Original Song for ENOCH Movie) Ft. Tee Worship Lyrics

Copyright © 2023 GMLyrics