Skip to content
Home » Hausa Hymns » Zo, Mu Yabi Ƙaunar Yesu

Zo, Mu Yabi Ƙaunar Yesu

  Zo, Mu Yabi Ƙaunar Yesu
  1) Zo, mu yabi ƙaunar Yesu,
  Jinƙansa da alherinsa.
  Yana shirya mana wuri
  Cikin Sama gun Uban.

  KORUS
  Can a Sama, wurin Yesu,
  Masu bi za su taru wurinsa
  Za mu rera waƙa,
  Mu yabi girman sunansa

  2) Lokacin da mu ke nan a duniya,
  Ƴar wahala mu ke sha,
  Amma ran da za mu Sama
  Farin ciki za mu yi.

  Korus

  3) Bi shi nan da dukan zuciya,
  Yi aniya cikin aikinsa.
  Za mu manta da wahala
  In mun shiga mulkinsa.

  4) Gaba dai, mu Masu Binsa,
  Har mu ga Mai Cetonmu.
  Wata rana ƙofar Sama
  Za ta buɗe dominmu.

  Korus

  Leave a Reply

  Your email address will not be published. Required fields are marked *