Skip to content
Home » Hausa Hymns » Yau Cikin Birnin Dauda An Haifa Mana Mai Ceto

Yau Cikin Birnin Dauda An Haifa Mana Mai Ceto

  Yau Cikin Birnin Dauda An Haifa Mana Mai Ceto

  1) Yau cikin Birnin Dauda an haifa mana Mai Ceto.
  Yau Yesu ya shigo duniya, Ɗan Allah mai girma.
  Cikin sakarkari an kwantadda shi.
  Shanu suna kallonsa, ana yabon mai girma.
  A can a Baitalahmi an haifi Kiristi
  Shi ne, shi ne maɗaukaki, Allah mai girma.

  2) Mala’ika fa yau ya zo gun makiyaya.
  Ya ce masu, Yau Kiristi Ɗan Allah ya iso.
  Annabawa sun yi annabcin zuwansa.
  Annabcinsu ya fi saninmu, Ɗan Allah ya iso.
  Mu je mu gaida jaririn nan mai ceto.
  Shi ne, shi ne, ɗan ragon Allah mai ceto.

  3) Yau mala’iku cikin sama suna ta yabo.
  Suna cewa Alhamdu ga AIIah a duni ya salama.
  Babban Sarki ne a duniyan nan duka.
  Ɗaukaka duka nasa ne, an haifa mana mai ceto.
  Halle-Halleluya Ɗan Allah, sabko.
  Yau ne an haifi wannan sarkin Yahudawa.

  4) Shehuna sun ga tamraron nan daga gabas.
  Yanzu a Baitalahmi sun ga tamraron nan,
  Sun zo sun durƙusa, suna ta yabo,
  Kayan zinariya ne suna zuba gun Yesu.
  Mu je mu kawo ziyaramu gun Yesu,
  Mu je, mu yabi jaririn nan mai ceto.

  5) Halleluya. Halleluya, Kiristi ya iso
  Aikakke ne shi, tilo ‘Dan Allah ya iso.
  Yahudawa suna ta jiran zuwansa.
  Har wa yau ba su sani yau ne Kiristi ya sabko
  Har yau suna ta jiran Kiristi mai ceto,
  Har yau suna ta duban hanyar mai ceto.

  Leave a Reply

  Your email address will not be published. Required fields are marked *