Skip to content
Home » Hausa Hymns » Ruhun iko, zo gare mu, Mun ga kasawarmu yau

Ruhun iko, zo gare mu, Mun ga kasawarmu yau

  Verse 1
  Ruhun iko, zo gare mu,
  Mun ga kasawarmu yau.
  Rashin jinkai, rashin kauna
  Rashin musun kanmu ma.

  Chorus
  Sai ka zo, ka tsarkake mu
  Daga dukan kasawa.
  Muna jira, muna jira
  Tsarkake mu duk yanzu.

  Verse 2
  Ruhun sani, zo gare mu,
  Akwai duhu cikinmu.
  Sanasshe mu, koya mana
  Hanyar tsarkakewar rai.

  Verse 3
  Ruhun wuta, zo gare mu,
  Kone duk muguntarmu
  Har mu zama mutanenka,
  Cikin dukan gaskiya.

  Verse 4
  Ruhun haske da addu’a,
  Bi da mu, ka karfafa.
  Muna bege, muna bege
  Har mu sami nasara.

  Verse 5
  Ruhun kauna, zo gare mu,
  Sai ka yafe mu yanzu.
  Muna jira, muna kuka,
  Amsa dai addu’armu.

  Verse 6
  ‘Yanuwa, ku yafa Yesu,
  Yafa sabon hali kuwa
  Yafa kuma zuciyar tausayi,
  Ladabi da jurewa.

  Verse 7
  Ruhun Kristi, ni na gode,
  Kana nan a zuciya,
  Mallake ni, mallake ni
  Daga yau har abada.

  Leave a Reply

  Your email address will not be published. Required fields are marked *