Skip to content
Home » Hausa Hymns » Ku Yi Ta Wa’azi Wurin Mutane Duk

Ku Yi Ta Wa’azi Wurin Mutane Duk

  Ku Yi Ta Wa’azi Wurin Mutane Duk

  1)Ku yi ta wa’azi wurin mutane duk,
  Gama a duniya akwai wahalar rai.
  Bari duk Masu Bi su shaida ko’ina,
  Mai Taimako ya zo.

  KORUS
  Mai Taimako ya zo, Mai Taimako ya zo,
  Ruhu Mai Tsarki da Allah ya aiko.
  Ku labartad da shi wurin mutane duk,
  Mai Taimako ya zo.

  2) Mun sami haskensa, ya watsa duhunmu,
  Ya kau da tsoro duk, ya ba mu kwanciyar rai.
  Ya kawo gafara ta dukan zunubi,
  Mai Taimako ya zo.

  Korus

  3) Ga Ubangijinmu, ya zo da warkarwa.
  Ga ƴaƴan duniya, ruɗaɗɗu na Shaiɗan.
  Ya kwance ɗaurarru, ya kawo fansarsu,
  Mai Taimako ya zo.

  Korus

  4) Ya Allah mai ƙauna, ko ni na iya ƙi
  In shaida j inƙanka ga dukan mutane?
  Ga ni da, matacce, ka ba ni sabon rai,
  Mai Taimako ya zo.

  Korus

  Leave a Reply

  Your email address will not be published. Required fields are marked *