Skip to content
Home » Hausa Hymns » A cikin duniyan nan yanzu

A cikin duniyan nan yanzu

  1) A cikin duniyan nan yanzu,
  Ya Ubanjiji, bi da mu.
  Akwai jaraba ko’ina,
  Ka bi da mu da Ruhunka.

  KORUS
  Ya Ubangiji, Mai Ceto,
  In ban da kai, ba taimako,
  Ka koya mana nufinka,
  Ka bi da mu da Ruhunka.

  2) Ga aiki yana jiranmu,
  Ga tumakinka, ƃatattu,
  Mu je mu kawo su yanzu,
  Ka bi da mu da Ruhunka.

  Korus
  3) In za mu shiga yaƙinka,
  Mu yi kokawa da magauta,
  Ka ƙarfafa ƴan yaƙinka
  Ka bi da mu da Ruhunka.

  Korus
  4) Idan mun gama aikinka,
  Ka kira mu ga hutawa.
  Ka bi da mu da Ruhunka,
  Ka kai mu Sama lafiya.

  Korus

  Leave a Reply

  Your email address will not be published. Required fields are marked *